25 Ka kawo Haruna da ɗansa, Ele'azara, bisa Dutsen Hor.
26 Ka tuɓe wa Haruna rigunansa na firist, ka sa wa ɗansa, Ele'azara. Haruna zai mutu can.”
27 Musa kuwa ya yi yadda Ubangiji ya umarta. Suka hau bisa Dutsen Hor a idon dukan taron jama'a.
28 Sai Musa ya tuɓe wa Haruna rigunansa na firist ya sa wa Ele'azara ɗan Haruna. Haruna kuwa ya rasu a kan dutsen. Sa'an nan Musa da Ele'azara suka sauko daga kan dutsen.
29 Sa'ad da dukan jama'a suka ga Haruna ya rasu, sai duka suka yi makoki dominsa har kwana talatin.