4 Don me ka fito da taron jama'ar Ubangiji zuwa cikin wannan jeji don mu mutu a nan, mu da dabbobinmu?
5 Don me kuma ka sa muka fito daga masar, ka kawo mu a wannan mugun wuri inda babu hatsi, ko ɓaure, ko inabi, ko rumman, ko ruwan da za a sha ma?”
6 Sai Musa da Haruna suka bar taron jama'a, suka tafi ƙofar alfarwa ta sujada, suka fāɗi rubda ciki. Ɗaukakar Ubangiji kuwa ta bayyana a gare su.
7 Ubangiji ya ce wa Musa,
8 “Ka ɗauki sandanka, kai da Haruna, ɗan'uwanka, ku tara jama'a, ku yi magana da dutsen a gabansu ya ba da ruwan da yake cikinsa. Za ka sa ruwa ya ɓuɓɓugo musu daga dutsen. Ta haka za ka ba taron jama'a da garkunansu ruwan sha.”
9 Musa kuwa ya ɗauki sanda daga gaban Ubangiji kamar yadda ya umarce shi.
10 Sai Musa da Haruna suka sa jama'a su taru a gaban dutsen, sa'an nan Musa ya ce musu, “Ku kasa kunne, ku 'yan tawaye, za mu fito muku da ruwa daga cikin dutsen nan?”