1 Sai Bal'amu ya ce wa Balak, “Ka gina mini bagadai guda bakwai a nan, ka kawo mini bijimai bakwai da raguna bakwai.”
2 Balak ya yi yadda Bal'amu ya faɗa masa. Balak da Bal'amu suka miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.
3 Sai Bal'amu ya ce wa Balak, “Tsaya kusa da hadayarka ta ƙonawa, ni kuwa zan tafi can, in ga ko Ubangiji zai sadu da ni. Duk abin da ya bayyana mini, zan faɗa maka.” Ya kuwa tafi wani faƙo a kan tudu.
4 Da Ubangiji ya sadu da Bal'amu, sai Bal'amu ya ce wa Ubangiji, “Na riga na shirya bagadai bakwai, na kuwa miƙa bijimi guda da rago guda a kan kowane bagade.”
5 Ubangiji kuwa ya sa magana a bakin Bal'amu ya ce, “Koma wurin Balak, ka faɗa masa abin da na faɗa maka.”
6 Sai ya koma wurin Balak, ya same shi da dukan dattawan Mowab suna tsaye kusa da hadayarsa ta ƙonawa.
7 Bal'amu kuwa ya faɗi jawabinsa, ya ce“Tun daga Aram Balak ya kawo ni,Shi Sarkin Mowab ne daga gabashin duwatsu.‘Zo, la'anta mini Yakubu,Zo, ka tsine wa Isra'ila!’