10 Wa zai iya ƙidaya yawan Isra'ilawa da suke kamar ƙura?Yawansu ya fi gaban lasaftawa.Bari ƙarshena ya zama kamar ɗaya daga cikin mutane Allah,Bari in mutu cikin salama kamar adalai.”
11 Sai Balak ya ce wa Bal'amu, “Me ke nan ka yi mini? Na kawo ka domin ka la'anta abokan gābana, ga shi, sai albarka kake sa musu!”
12 Bal'amu kuwa ya ce, “Ai, ba tilas ne in hurta abin da Ubangiji ya sa a bakina ba?”
13 Sai Balak ya ce masa, “Zo, mu tafi wani wuri inda za ka gan su. Waɗanda suka fi kusa kaɗai ne za ka gani, amma ba za ka iya ganinsu duka ba. Ka la'anta mini su daga can.”
14 Ya kuwa kai shi saurar Zofim a bisa Dutsen Fisga. Sa'an nan ya gina bagadai bakwai, ya miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.
15 Sai Bal'amu ya ce wa Balak, “Tsaya nan kusa da hadayarka ta ƙonawa, ni kuwa in tafi in sadu da Ubangiji a can.”
16 Ubangiji kuwa ya sadu da Bal'amu ya sa masa magana a baka, ya ce, “Koma wurin Balak ka faɗa masa abin da na faɗa maka.”