27 Sai Balak ya ce wa Bal'amu, “In ka yarda ka zo in kai ka wani wuri, watakila Allah zai yarda ka la'anta mini su a can.”
28 Balak kuwa ya kai Bal'amu a ƙwanƙolin Dutsen Feyor wanda yake fuskantar hamada.
29 Sai Bal'amu ya ce wa Balak, “Ka gina mini bagadai bakwai, ka shirya mini bijimai bakwai da raguna bakwai.”
30 Balak ya yi yadda Bal'amu ya faɗa masa. Ya miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.