1 Sa'ad da Isra'ilawa suka yi zango a Shittim, maza suka fara yin lalata da matan Mowabawa.
2 Waɗannan mata sukan gayyaci mutanen zuwa wajen shagalin tsafinsu. Isra'ilawa kuwa sukan ci abinci, su kuma yi sujada ga gumaka.
3 Ta haka Isra'ilawa suka shiga bautar gumakan Ba'al na Feyor. Sai Ubangiji ya husata da Isra'ilawa.
4 Ya ce wa Musa, “Ɗauki sugabannin jama'a, ka rataye su a rana a gabana don in huce daga fushin da nake yi da Isra'ilawa.”