3 Ta haka Isra'ilawa suka shiga bautar gumakan Ba'al na Feyor. Sai Ubangiji ya husata da Isra'ilawa.
4 Ya ce wa Musa, “Ɗauki sugabannin jama'a, ka rataye su a rana a gabana don in huce daga fushin da nake yi da Isra'ilawa.”
5 Musa kuwa ya ce wa alƙalan Isra'ilawa, “Kowa ya kashe mutanensa da suka shiga bautar gumakan Ba'al-feyor.”
6 Sai ga wani Ba'isra'ile ya taho da wata mace, Bamadayaniya, ya kai ta alfarwarsa ƙiriƙiri a gaban Musa da dukan taron jama'ar Isra'ila a sa'ad da suke kuka a ƙofar alfarwa ta sujada.
7 Finehas ɗan Ele'azara, wato jikan Haruna, firist, ya gani, sai ya tashi daga cikin taron, ya ɗauki mashi.
8 Ya bi Ba'isra'ilen, har zuwa ƙuryar alfarwar, ya soke dukansu biyu, Ba'isra'ilen da macen, har ya sha zarar macen. Da haka aka tsai da annoba daga Isra'ilawa.
9 Duk da haka annobar ta kashe mutane dubu ashirin da dubu huɗu (24,000).