6 Sai ga wani Ba'isra'ile ya taho da wata mace, Bamadayaniya, ya kai ta alfarwarsa ƙiriƙiri a gaban Musa da dukan taron jama'ar Isra'ila a sa'ad da suke kuka a ƙofar alfarwa ta sujada.
7 Finehas ɗan Ele'azara, wato jikan Haruna, firist, ya gani, sai ya tashi daga cikin taron, ya ɗauki mashi.
8 Ya bi Ba'isra'ilen, har zuwa ƙuryar alfarwar, ya soke dukansu biyu, Ba'isra'ilen da macen, har ya sha zarar macen. Da haka aka tsai da annoba daga Isra'ilawa.
9 Duk da haka annobar ta kashe mutane dubu ashirin da dubu huɗu (24,000).
10 Sai Ubangiji ya ce wa Musa,
11 “Finehas ɗan Ele'azara, wato jikan Haruna, firist, ya kawar da fushina daga Isra'ilawa saboda ya yi kishi irin nawa a gabansu, don haka ban shafe Isra'ilawa saboda kishina ba.
12 Domin haka ina yi masa alkawarin da ba zai ƙare ba.