12 'Ya'yan Saminu, maza, bisa ga iyalansu, su ne Yemuwel, da Yamin, da Yakin,
13 da Zohar, da Shawul. Waɗannan su ne iyalan kabilar Saminu.
14 Yawansu ya kai mutum dubu ashirin da biyu da ɗari biyu (22,200).
15 Zuriyar Gad bisa ga iyalansu, su ne Zifiyon, da Haggi, da Shuni,
16 da Ezbon, da Eri,
17 da Arodi, da Areli.
18 Waɗannan su ne iyalan kabilar Gad. Yawan mutanensu ya kai dubu arba'in da ɗari biyar (40,500).