15 Zuriyar Gad bisa ga iyalansu, su ne Zifiyon, da Haggi, da Shuni,
16 da Ezbon, da Eri,
17 da Arodi, da Areli.
18 Waɗannan su ne iyalan kabilar Gad. Yawan mutanensu ya kai dubu arba'in da ɗari biyar (40,500).
19 Kabilar Yahuza ke nan, (Er, da Onan, 'ya'yan Yahuza sun mutu a ƙasar Kan'ana).
20 Sauran 'ya'yansa bisa ga iyalansu su ne, Shela, da Feresa, da Zera,
21 da Hesruna, da Hamul.