17 da Arodi, da Areli.
18 Waɗannan su ne iyalan kabilar Gad. Yawan mutanensu ya kai dubu arba'in da ɗari biyar (40,500).
19 Kabilar Yahuza ke nan, (Er, da Onan, 'ya'yan Yahuza sun mutu a ƙasar Kan'ana).
20 Sauran 'ya'yansa bisa ga iyalansu su ne, Shela, da Feresa, da Zera,
21 da Hesruna, da Hamul.
22 Waɗannan su ne iyalan kabilar Yahuza. Yawan mutanensu ya kai dubu saba'in da shida da ɗari biyar (76,500).
23 Kabilar Issaka ke nan bisa ga iyalansu, da Tola, da Fuwa,