33 Zelofehad, ɗan Hefer, ba shi da 'ya'ya maza, sai dai 'ya'ya mata. Sunayen 'ya'yansa mata su ne Mala, da Nowa, da Hogla, da Milka, da Tirza.
34 Waɗannan su ne iyalan kabilar Manassa. Yawansu ya kai mutum dubu hamsin da biyu da ɗari bakwai (52,700).
35 Waɗannan su ne kabilar Ifraimu bisa ga iyalansu, Shutela, da Beker, da Tahat.
36 Iyalin Eran suna lasafta kansu, daga zuriyar Shutela ne.
37 Waɗannan su ne iyalan kabilar Ifraimu. Yawansu ya kai dubu talatin da biyu da ɗari biyar (32,500).
38 Kabilar Biliyaminu ke nan bisa ga iyalansu, Bela, da Ashbel, da Ahiram,
39 da Shuffim, da Huffim.