50 Waɗannan su ne iyalan kabilar Naftali. Yawansu ya kai mutum dubu arba'in da biyar da ɗari huɗu (45,400).
51 Jimillar Isra'ilawa maza waɗanda aka ƙidaya, dubu ɗari shida da dubu ɗaya da ɗari bakwai da talatin (601,730).
52 Sai Ubangiji ya ce wa Musa,
53 “A raba wa waɗannan mutane gādon ƙasar bisa ga yawan kowace kabila.
54 Za ka ba babbar kabila babban rabo, ka ba ƙaramar kabila ƙaramin rabo. Kowace kabila za a ba ta gādo bisa ga yawanta.
55 Amma za a rarraba musu gādon ƙasar kabila kabila ta hanyar kuri'a.
56 Za a rarraba gādo tsakanin manya da ƙananan kabilai ta hanyar kuri'a.”