52 Sai Ubangiji ya ce wa Musa,
53 “A raba wa waɗannan mutane gādon ƙasar bisa ga yawan kowace kabila.
54 Za ka ba babbar kabila babban rabo, ka ba ƙaramar kabila ƙaramin rabo. Kowace kabila za a ba ta gādo bisa ga yawanta.
55 Amma za a rarraba musu gādon ƙasar kabila kabila ta hanyar kuri'a.
56 Za a rarraba gādo tsakanin manya da ƙananan kabilai ta hanyar kuri'a.”
57 Waɗannan su ne Lawiyawan da aka ƙidaya bisa ga iyalansu, Gershon, da Kohat, da Merari.
58 Sauran iyalin Lawiyawa daga zuriyar Libni ne, da Hebron, da Mali, da Mushi, da Kora. Kohat shi ne mahaifin Amram,