20 Ka danƙa masa ikonka don taron jama'ar Isra'ila su yi masa biyayya.
21 Zai dogara ga Ele'azara, firist, don ya san nufina, ta wurin amfani da Urim da Tummin. Ta haka ne Ele'azara zai bi da Joshuwa da dukan taron jama'ar Isra'ila cikin al'amuransu.”
22 Musa kuwa ya yi kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. Ya ɗauki Joshuwa, ya sa shi ya tsaya a gaban Ele'azara, firist, da gaban dukan taron.
23 Ya ɗibiya hannuwansa a kansa, ya keɓe shi kamar yadda Ubangiji ya umarta.