9 Idan kuwa ba shi da 'ya, sai a ba 'yan'uwansa gādonsa.
10 Idan kuma ba shi da 'yan'uwa, sai a ba 'yan'uwan mahaifinsa gādonsa.
11 Idan kuma ba shi da su, sai a ba danginsa na kusa su mallaka, wannan zai zama umarni da ka'ida ga Isra'ilawa kamar yadda ni, Ubangiji na umarce ka.’ ”
12 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Hau bisa kan Dutsen Abarim, ka dubi ƙasa wadda na ba Isra'ilawa.
13 Bayan da ka gan ta, za ka mutu kamar yadda Haruna ya yi,
14 domin ba ku yi biyayya da umarnina ba a jejin Zin. Lokacin da dukan jama'a suka yi mini gunaguni a Meriba, ba ku nuna ikona mai tsarki a gabansu ba.” (Wannan shi ne ruwan Meriba na Kadesh a jejin Zin.)
15 Musa kuwa ya ce wa Ubangiji,