7 Hadaya ta sha za ta zama rubu'in moɗa na ruwan inabi domin kowane ɗan rago. Za a kwarara hadaya ta sha mai gafi ga Ubangiji a bagade.
8 Ɗayan ɗan ragon kuma za a miƙa da maraice, tare da hadaya ta gari kamar ta safe, da hadayarsa ta sha. Za a miƙa shi hadaya ta ƙonawa, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
9 A rana Asabar kuwa za a miƙa 'yan raguna biyu bana ɗaya ɗaya marasa lahani da mudu biyu na lallausan gari, kwaɓaɓɓe da mai, domin yin hadaya ta gari tare da hadayarsa ta sha.
10 Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa ta kowace ranar Asabar, banda hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadaya ta sha.
11 A farkon kowane wata sai a miƙa hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, da 'yan bijimai biyu, da rago ɗaya, da kuma 'yan raguna bakwai bana daya daya; marasa lahani,
12 hadaya ta gari kuma, a kwaɓa gari humushi uku na garwa da man zaitun don kowane bijimi, da gari humushi biyu na garwa don rago,
13 da kuma gari humushin garwa don ɗan rago. Waɗannan su ne hadayu na abinci na ƙonawa, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.