1 A rana ta fari ga wata na bakwai za a taru domin yin sujada, ba za a yi aiki a ranar ba. A ranar za a busa ƙahoni.
2 Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, da rago guda, da 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Dabbobin za su zama marasa lahani.
3 Tare da dabbobin za a kuma miƙa hadaya ta lallausan gāri kwaɓaɓɓe da mai. Za a miƙa gāri humushi uku na garwa tare da bijimin, humushi biyu na garwa kuma tare da ragon.
4 Za a miƙa humushin garwa na gāri tare da kowane ɗan rago.
5 Sai kuma a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi domin a yi kafara.
6 Banda waɗannan hadayu kuma, sai a miƙa hadaya ta ƙonawa tare da hadayarta ta gari, da akan yi a tsayawar wata, da kuma hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri, da hadayarsu ta sha. Sai a yi su bisa ga ka'idar yinsu. Hadaya ke nan da akan yi da wuta don daɗin ƙanshi ga Ubangiji.