32 A rana ta bakwai ta idin za a miƙa bijimai bakwai, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dabbobin su zama marasa lahani.
33 Za a kuma miƙa hadaya ta gāri da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar.
34 Za a kuma miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.
35 A rana ta takwas za a taru domin yin sujada. Ba za a yi aiki ba.
36 Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi, da rago, da 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Dabbobin su zama marasa lahani.
37 Za a miƙa hadaya ta gāri da hadaya ta sha tare da bijimin, da ragon, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar.
38 Za a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.