17 Waɗannan su ne 'ya'yan Lawi, maza, bisa ga sunayensu, da Gershon, da Kohat, da Merari.
18 Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Gershon, maza, bisa ga iyalansu, Libni da Shimai.
19 Ga 'ya'yan Kohat, maza, bisa ga iyalansu, da Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel.
20 Ga kuma 'ya'yan Merari, maza, bisa ga iyalansu, da Mali da Mushi. Waɗannan su ne iyalan Lawi bisa ga gidajen kakanninsu.
21 Iyalin Libnawa, da na Shimaiyawa su ne iyalan Gershon.
22 Jimillarsa tun daga ɗa namiji mai wata ɗaya zuwa gaba, mutum dubu bakwai ne da ɗari biyar (7,500).
23 Iyalan Gershonawa za su yi zango a bayan alfarwar daga yamma.