21 Iyalin Libnawa, da na Shimaiyawa su ne iyalan Gershon.
22 Jimillarsa tun daga ɗa namiji mai wata ɗaya zuwa gaba, mutum dubu bakwai ne da ɗari biyar (7,500).
23 Iyalan Gershonawa za su yi zango a bayan alfarwar daga yamma.
24 Eliyasaf, ɗan Layel, shi ne shugaban gidan kakanninsa, Gershonawa.
25 'Ya'yan Gershon, maza, su ne da aikin lura da alfarwa ta sujada da murfinta na ciki da na waje, da labulen ƙofar,
26 da labulen farfajiyar da yake kewaye da alfarwar, da bagade, da labulen ƙofar farfajiyar. Su za su lura da dukan aikin da ya shafi waɗannan abubuwa.
27 Iyalan Kohat su ne iyalin Amramawa, da na Izharawa, da na Hebronawa, da na Uzziyelawa. Waɗannan su ne iyalan Kohatawa.