3 Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Haruna, maza, da aka naɗa firistoci domin su yi aikin firist.
4 Amma Nadab da Abihu sun mutu a gaban Ubangiji a jejin Sinai, a sa'ad da suka ƙona turare da haramtacciyar wuta. Sun mutu, ba su da 'ya'ya, saboda haka Ele'azara da Itamar suka yi aikin firist su kaɗai a zamanin mahaifinsu Haruna.
5 Ubangiji ya ce wa Musa,
6 “Kawo kabilar Lawiyawa kusa, ka sa su su yi aiki tare da Haruna, firist.
7 Sai su yi wa firistoci da dukan jama'a aiki a gaban alfarwa ta sujada.
8 Su za su lura da kayayyakin alfarwa ta sujada su kuma yi wa Isra'ilawa aiki.
9 Abin da Lawiyawa za su yi, shi ne su yi wa Haruna da 'ya'yansa aiki.