34 Yawan mazajensu duka da aka ƙidaya tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba, mutum dubu shida ne da ɗari biyu (6,200).
35 Shugaban gidan kakannin iyalan Merari kuwa shi ne Zuriyel, ɗan Abihail. Za su kafa zangonsu a arewacin alfarwar.
36 Aikin da aka danƙa wa 'ya'yan Merari shi ne lura da katakan alfarwar, da sanduna, da dirkoki, da kwasfa, da sauran abubuwa duka, da duk ayyukan da suka shafi waɗannan,
37 da kuma dirkoki na farfajiyar da ta kewaye wurin, da kwasfa da turaku da igiyoyinsu.
38 Waɗanda za su yi zango a gaban alfarwa ta sujada daga gabas, su ne Musa, da Haruna da 'ya'yansa maza, waɗanda aka danƙa musu tafiyar da aikin Wuri Mai Tsarki, da dukan aikin da za a yi wa Isra'ilawa. Banda su, duk wanda ya je kusa da wurin sai a kashe shi.
39 Dukan Lawiyawa waɗanda Musa da Haruna suka ƙidaya bisa ga iyalansu, bisa ga umarnin Ubangiji, tun daga mai wata ɗaya zuwa gaba, mazaje dubu ashirin da dubu biyu ne (22,000).
40 Sai kuma Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ƙidaya dukan 'ya'yan fari maza na Isra'ilawa, tun daga wata ɗaya zuwa mai gaba, ka rubuta sunayensu.