5 Ubangiji ya ce wa Musa,
6 “Kawo kabilar Lawiyawa kusa, ka sa su su yi aiki tare da Haruna, firist.
7 Sai su yi wa firistoci da dukan jama'a aiki a gaban alfarwa ta sujada.
8 Su za su lura da kayayyakin alfarwa ta sujada su kuma yi wa Isra'ilawa aiki.
9 Abin da Lawiyawa za su yi, shi ne su yi wa Haruna da 'ya'yansa aiki.
10 Ka sa Haruna da 'ya'yansa maza, su kula da aikinsu na firist, idan kuwa wani mutum dabam ya yi ƙoƙarin yin wannan aiki, to, za a kashe shi.”
11 Ubangiji kuma ya ce wa Musa,