40 'Yan mata dubu goma sha shida (16,000), daga ciki aka fitar da 'yan mata talatin da biyu domin Ubangiji.
41 Sai Musa ya ba Ele'azara firist rabon Ubangiji, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.
42 Wannan shi ne kashin da aka ba jama'ar Isra'ila cikin kashin da aka ware daga na waɗanda suka tafi yaƙin.
43 Tumaki dubu ɗari uku da talatin da bakwai da ɗari bayar (337,500),
44 shanu dubu talatin da dubu shida (36,000),
45 jakai dubu talatin da ɗari biyar (30,500),
46 'yan mata dubu goma sha shida (16,000).