16 Sai suka zo kusa da shi, suka ce, “Za mu gina garu na dutse don mu kāre dabbobinmu, da birane don 'ya'yanmu a nan.
17 'Ya'yanmu za su zauna a biranen don gudun mazaunan ƙasar, amma mu za mu ɗauki makamai mu tafi tare da sauran Isra'ilawa, har mu kai su wuraren zamansu.
18 Ba kuwa za mu koma gidajenmu ba, sai lokacin da kowane Ba'isra'ile ya sami gādonsa.
19 Gama ba za mu ci gādo tare da su a wancan hayin Urdun ba, domin mun sami gādonmu a wannan hayi na gabashin Urdun.”
20 Sai Musa ya ce musu, “Idan za ku yi haka, wato ku ɗauki makamai, ku tafi yaƙi a gaban Ubangiji,
21 kowane sojanku ya haye Urdun a gaban Ubangiji, har lokacin da Ubangiji ya kori abokan gābansa daga gabansa,
22 har kuma lokacin da aka ci ƙasar a gaban Ubangiji kafin ku koma, to, za ku kuɓuta daga alhakinku a gaban Ubangiji da jama'ar Isra'ila. Wannan ƙasa kuwa za ta zama mallakarku a gaban Ubangiji.