31 Gadawa da Ra'ubainawa kuwa suka ce, “Kamar yadda Ubangiji ya ce wa barorinka, haka za mu yi.
32 Za mu haye da shirin yaƙi a gaban Ubangiji zuwa cikin ƙasar Kan'aniyawa, amma za mu sami gādonmu a wannan hayin Urdun.”
33 Sa'an nan Musa ya ba Gadawa, da Ra'ubainawa, da rabin mutanen Manassa, ɗan Yusufu, mulkin Sihon, Sarkin Amoriyawa, da mulkin Og, Sarkin Bashan, wato ƙasar da biranenta da karkaransu.
34 Sai Gadawa suka gina Dibon, da Atarot, da Arower,
35 da Atarot-shofan, da Yazar, da Yogbeha,
36 da Bet-nimra, da Bet-aram su zama birane masu garu da shinge don dabbobi.
37 Ra'ubainawa kuwa suka gina Heshbon da Eleyale, da Kiriyatayim,