10 Suka tashi daga Elim, suka sauka a gefen Bahar Maliya.
11 Da suka tashi daga Bahar Maliya suka sauka a jejin Sin.
12 Suka tashi daga jejin Sin, suka sauka a Dofka.
13 Daga Dofka suka tafi Alush.
14 Suka tashi daga Alush suka sauka a Refidim inda mutane suka rasa ruwan sha.
15 Suka tashi daga Refidim suka sauka a jejin Sinai.
16 Da suka tashi daga jejin Sinai, sai suka sauka a Kibrot-hata'awa.