28 Suka kama hanya daga Tara suka sauka a Mitka.
29 Suka kuma kama hanya daga Mitka suka sauka a Hashmona.
30 Daga Hashmona suka sauka a Moserot.
31 Da suka tashi daga Moserot suka sauka a Bene-ya'akan.
32 Suka tashi daga Bene-ya'akan suka sauka a Hor-hagidgad.
33 Da suka tashi daga Hor-hagidgad suka sauka a Yotbata.
34 Suka kama hanya daga Yotbata suka sauka a Abrona.