35 Da suka tashi daga Abrona, sai suka sauka a Eziyon-geber.
36 Suka tashi daga Eziyon-geber suka sauka a jejin Zin, wato Kadesh.
37 Da suka kama hanya daga Kadesh suka sauka a Dutsen Hor a kan iyakar ƙasar Edom.
38 Bisa ga umarnin Ubangiji, Haruna firist ya hau Dutsen Hor inda ya rasu a rana ta fari ga watan biyar a shekara ta arba'in ta fitowar jama'ar Isra'ila daga ƙasar Masar.
39 Haruna yana da shekara ɗari da ashirin da uku sa'ad da ya rasu a Dutsen Hor.
40 Sai Sarkin Arad, Bakan'ane wanda yake zaune a Negeb, a ƙasar Kan'ana, ya ji zuwan Isra'ilawa.
41 Isra'ilawa kuma suka tashi daga Dutsen Hor, suka sauka a Zalmona.