6 Suka tashi daga Sukkot suka sauka a Etam wadda take a gefen jejin.
7 Da suka tashi daga Etam, sai suka juya zuwa Fi-hahirot wadda take gaban Ba'al-zefon suka sauka a gaban Migdol.
8 Da suka tashi daga gaban Fi-hahirot sai suka haye teku zuwa cikin jejin. Suka yi tafiya kwana uku a jejin Etam, suka sauka a Mara.
9 Suka tashi daga Mara suka zo Elim inda akwai maɓuɓɓugan ruwa guda goma sha biyu da itacen dabino guda saba'in. Sai suka sauka a can.
10 Suka tashi daga Elim, suka sauka a gefen Bahar Maliya.
11 Da suka tashi daga Bahar Maliya suka sauka a jejin Sin.
12 Suka tashi daga jejin Sin, suka sauka a Dofka.