17 “Ga sunayen mutanen da za su taimake ka raba gādon ƙasar, Ele'azara firist, da Joshuwa ɗan Nun.
18 Za ka kuma ɗauki shugaba ɗaya daga kowace kabila don su raba gādon ƙasar.
19 Waɗannan su ne sunayen mutanen, Kalibu ɗan Yefunne daga kabilar Yahuza.
20 Shemuyel ɗan Ammihud daga kabilar Saminu.
21 Elidad ɗan Kislon daga kabilar Biliyaminu.
22 Bukki ɗan Yogli daga kabilar Dan.
23 Na wajen Yusufu, Haniyel ɗan Efod daga kabilar Manassa,