3 Iyakar ƙasarsu daga wajen kudu ta miƙa tun daga wajen jejin Zin, har zuwa iyakar Edom. Iyakarsu kuwa ta wajen kudu za ta fara daga ƙarshen Tekun Gishiri wajen gabas.
4 Sa'an nan kuma za ta nausa ta nufin hawan Akrabbim, ta ƙetare zuwa Zin, ta dangana da kudancin Kadesh-barneya, sa'an nan ta miƙa zuwa Hazar'addar, ta zarce ta bi ta Azemon.
5 Iyakar za ta nausa daga Azemon zuwa rafin Masar, ta fāɗa bahar.
6 Bahar Rum ita ce iyakarsu ta wajen yamma.
7 Iyakarsu a wajen arewa kuwa ita ce tun daga Bahar Rum zuwa Dutsen Hor.
8 Daga Dutsen Hor iyakar za ta bi zuwa Hamat ta tsaya a Zedad.
9 Iyakar za ta miƙa har zuwa Zifron, ta tsaya a Hazar-enan, wannan ita ce iyakarsu a wajen arewa.