6 Bahar Rum ita ce iyakarsu ta wajen yamma.
7 Iyakarsu a wajen arewa kuwa ita ce tun daga Bahar Rum zuwa Dutsen Hor.
8 Daga Dutsen Hor iyakar za ta bi zuwa Hamat ta tsaya a Zedad.
9 Iyakar za ta miƙa har zuwa Zifron, ta tsaya a Hazar-enan, wannan ita ce iyakarsu a wajen arewa.
10 Iyakarsu a wajen gabas za ta tashi tun daga Haza-enan har zuwa Shefam.
11 Sa'an nan za ta gangara daga Shefam zuwa Ribla wajen gabashin Ayin. Za ta kuma gangara har ta kai Tekun Galili a wajen gabas.
12 Iyakar kuma za ta gangara har zuwa Urdun, ta tsaya a Tekun Gishiri. Wannan ita ce ƙasarsu da iyakokinta kewaye da ita.