15 Waɗannan birane shida za su zama wuraren mafaka ga jama'ar Isra'ila, da baƙi, da baren da yake zaune tare da su, domin duk wanda ya kashe wani ba da niyya ba, ya tsere zuwa can.
16 “Amma idan wani ya bugi wani da makami na ƙarfe har ya mutu, ya yi kisankai, sai a kashe shi.
17 Idan kuwa ya jefe shi da dutsen da ya isa a yi kisankai da shi, har ya mutu, ya yi kisankai ke nan, to, sai a kashe shi.
18 Idan kuwa ya buge shi da makami na itace da ya isa a yi kisankai da shi, har kuwa ya mutu, ya yi kisankai ka nan, sai a kashe shi.
19 Sai mai bin hakkin jinin ya kashe mai kisankan sa'ad da ya iske shi.
20 “Idan saboda ƙiyayya ya laɓe, ya soke shi, ko ya jefe shi har ya mutu,
21 ko kuma saboda ƙiyayya ya naushe shi da hannu har ya mutu, sai a kashe shi, gama ya yi kisankai ke nan. Wanda yake bin hakkin jinin, zai kashe wanda ya yi kisankai sa'ad da ya iske shi.