23 ko ya jefe shi da dutsen da ya isa a kashe mutum da shi, ba da saninsa ba, shi kuwa ba maƙiyinsa ba ne, bai kuwa yi niyya ya cuce shi ba, amma ga shi kuwa, ya kashe shi,
24 to, sai taron jama'a su hukunta tsakanin mai kisankan da mai bin hakkin jinin bisa ga waɗannan ka'idodi.
25 Taron jama'a za su ceci mai kisankan daga hannun mai bin hakkin jinin. Su komar da shi a birnin mafaka inda ya je neman mafaka. Zai zauna can sai lokacin da babban firist da aka keɓe da tsattsarkan mai ya rasu.
26 Amma idan a wani lokaci mai kisankan ya fita kan iyakar birnin mafaka inda yake,
27 idan mai bin hakkin jinin ya same shi a bayan iyakar birnin, ya kashe shi, bai yi laifi ba.
28 Gama dole ne mai kisankan ya zauna cikin birnin mafaka inda yake, sai bayan rasuwar babban firist. Bayan rasuwar babban firist, mai kisankan yana iya komawa ƙasarsa.”
29 “Waɗannan ka'idodi sun shafe ku da zuriyarku a duk inda kuke.