1 Ubangiji ya faɗa wa Musa da Haruna,
2 su ƙidaya 'ya'yan Kohat, maza, daga cikin 'ya'yan Lawi bisa ga iyalansu da gidajen kakanninsu,
3 su ƙidaya daga mai shekara talatin zuwa hamsin, wato waɗanda suka isa su yi aiki a alfarwa ta sujada.
4 Wannan shi ne aikin 'ya'yan Kohat, maza, a cikin alfarwa ta sujada a kan abubuwa mafi tsarki.
5 Sa'ad da za a tashi daga zango, sai Haruna, tare da 'ya'yansa maza, su shiga cikin alfarwa, su kwance labulen kāriya, su rufe akwatin alkawari da shi.