4 Wannan shi ne aikin 'ya'yan Kohat, maza, a cikin alfarwa ta sujada a kan abubuwa mafi tsarki.
5 Sa'ad da za a tashi daga zango, sai Haruna, tare da 'ya'yansa maza, su shiga cikin alfarwa, su kwance labulen kāriya, su rufe akwatin alkawari da shi.
6 Sa'an nan kuma su rufe shi da fatun awaki, su kuma shimfiɗa shuɗin zane a bisansa, su zura masa sandunansa.
7 Sai su shimfiɗa shuɗin zane a kan tebur na gurasar ajiyewa, sa'an nan su dībiya farantai, da cokula, da kwanonin, da butocin hadaya ta sha, da gurasar ajiyewa.
8 Sa'an nan su rufe su da jan zane, a kuma rufe su da fatun awaki, sa'an nan su zura masa sandunansa.
9 Su kuma ɗauki shuɗin zane su rufe alkuki, da fitilunsa, da hantsukansa, da farantansa, da dukan kwanonin man da akan zuba masa.
10 Sai su sa alkukin da dukan kayayyakinsa a cikin fatar awaki su naɗe, su sarƙafa shi asandan ɗaukarsa.