28 Amma idan matar ba ta ƙazantar da kanta ba, ita tsattsarka ce, za ta kuɓuta, har ta haifi 'ya'ya.
29 Wannan ita ce dokar kishi idan mutum yana shayin matarsa, wai wani yana kwana da ita.
30 Matar kuwa za ta tsaya a gaban Ubangiji, firist kuwa zai yi da ita bisa ga wannan doka duka.
31 Mijin zai kuɓuta daga muguntar, amma matar za ta ɗauki muguntarta, idan ta yi laifin.