1 Ubangiji kuma ya umarci Musa
2 ya faɗa wa Isra'ilawa, cewa idan mace ko namiji ya ɗau wa'adi na musamman na zama keɓaɓɓe domin ya keɓe kansa ga Ubangiji,
3 sai ya keɓe kansa daga ruwan inabin da yake sa maye da ruwan inabi mai tsami. Kada kuma ya sha ruwan inabi mai tsami da yake sa maye da kowane irin abin sha da aka yi da 'ya'yan inabi mai tsami. Kada kuma ya ci ɗanyu ko busassun 'ya'yan inabi.
4 A dukan kwanakin nan da ya keɓe kansa, kada ya ci kowane irin abu da aka yi da kurangar inabi, ko da ƙwayar inabi ko da ɓawonsa.