11 Sai firist ya miƙa ɗaya don hadayar zunubi, ɗaya kuma don hadayar ƙonawa, ya yi kafara dominsa, gama ya yi zunubi saboda gawa. A wannan rana zai sāke keɓe kansa.
12 Sai ya sāke keɓe kansa ga Ubangiji daidai da kwanakin da ya ɗauka a dā. Zai kawo ɗan rago bana ɗaya na yin hadaya don laifi. Kwanakin da ya yi a dā ba su cikin lissafi domin keɓewarsa ta dā ta ƙazantu.
13 Wannan ita ce ka'idar zama keɓaɓɓe a ranar da keɓewarsa ta cika. Za a kai shi ƙofar alfarwa ta sujada,
14 ya miƙa wa Ubangiji hadayarsa ta ɗan rago bana ɗaya mara lahani don yin hadaya ta ƙonawa, da 'yar tunkiya bana ɗaya marar lahani ta yin hadaya don zunubi, da rago marar lahani don yin hadaya ta salama,
15 da kwandon abinci marar yisti da aka yi da lallausan gari kwaɓaɓɓe da mai, da ƙosai wanda aka yayyafa masa mai, da hadaya ta gari, da hadayu na sha.
16 Sai firist ɗin ya kai su gaban Ubangiji, ya miƙa hadaya don zunubi, da hadaya ta ƙonawa.
17 Ya kuma miƙa rago don hadaya ta salama ga Ubangiji tare da kwandon abinci, da ƙosai. Firist ɗin kuma zai miƙa hadaya ta gari, da hadaya ta sha.