21 Wannan ita ce ka'ida a kan keɓaɓɓe wanda ya ɗau wa'adi. Hadayarsa ga Ubangiji za ta zama bisa ga keɓewarsa, banda kuma abin da ya iya bayarwa. Sai ya cika wa'adin da ya ɗauka bisa ga ka'idar keɓewarsa.
22 Ubangiji ya umarci Musa
23 ya faɗa wa Haruna da 'ya'yansa maza, su sa wa Isra'ilawa albarka haka, su ce musu,
24 “Ubangiji ya sa muku albarka, ya kiyaye ku.
25 “Ubangiji ya sa fuskarsa ta haskaka ku, ya yi muku alheri.
26 “Ubangiji ya dube ku da idon rahama, ya ba ku salama.”
27 Idan suka sa wa jama'a wannan albarka sa'ad da suke addu'a ga Ubangiji domin Isra'ilawa, Ubangiji zai sa musu albarka.