1 Ubangiji kuwa ya ce wa Musa ya
2 faɗa wa Haruna cewa, “Sa'ad da za ka kakkafa fitilun nan bakwai, sai ka kakkafa su yadda za su haskaka sashin gaba.”
3 Haka kuwa Haruna ya yi. Ya kakkafa fitilun yadda za su haskaka a gaban alkukin, kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.
4 Da zinariya aka ƙera alkukin tun daga samansa har gindinsa, bisa ga fasalin da Ubangiji ya nuna wa Musa.