13 “Za ka keɓe Lawiyawa su zama kamar hadaya ta kaɗawa gare ni, ka sa Haruna da 'ya'yansa maza su lura da su.
14 Da haka za ka keɓe Lawiyawa daga cikin Isra'ilawa su zama nawa.
15 Bayan da ka tsarkake su, ka miƙa su kamar hadaya ta kaɗawa, za su cancanta su yi aiki a alfarwa ta sujada.
16 Gama dukansu an ba ni su daga cikin Isra'ilawa a maimakon dukan waɗanda suka fara buɗe mahaifa, wato dukan 'ya'yan farin Isra'ilawa. Na karɓi Lawiyawa su zama nawa.
17 A ranar da na kashe 'ya'yan fari na ƙasar Masar, na keɓe wa kaina dukan 'ya'yan fari na Isra'ilawa, na mutum, da na dabba.
18 Na kuwa keɓe wa kaina Lawiyawa a maimakon dukan 'ya'yan fari na Isra'ilawa.
19 Daga cikin Isra'ilawa kuwa na ba da Lawiyawa ga Haruna da 'ya'yansa maza don su yi wa Isra'ilawa hidima a alfarwa ta sujada, su kuma yi kafara dominsu don kada annoba ta sami Isra'ilawa sa'ad da suka kusaci alfarwa ta sujada.”