1 Sai Ubangiji ya yi wa Musa magana a jejin Sinai a watan farko na shekara ta biyu bayan fitarsu daga ƙasar Masar, ya ce,
2 “Sai Isra'ilawa su kiyaye Idin Ƙetarewa a ƙayyadadden lokacinsa.
3 A rana ta goma sha huɗu ga wannan wata, da maraice za su kiyaye shi a ƙayyadadden lokacinsa bisa ga dokokinsa da ka'idodinsa duka.”
4 Musa kuwa ya faɗa wa Isra'ilawa su kiyaye Idin Ƙetarewa.
5 Sai suka kiyaye Idin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu ga watan farko da maraice a cikin jejin Sinai bisa ga dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa. Haka kuwa Isra'ilawa suka yi.