3 A rana ta goma sha huɗu ga wannan wata, da maraice za su kiyaye shi a ƙayyadadden lokacinsa bisa ga dokokinsa da ka'idodinsa duka.”
4 Musa kuwa ya faɗa wa Isra'ilawa su kiyaye Idin Ƙetarewa.
5 Sai suka kiyaye Idin Ƙetarewa a rana ta goma sha huɗu ga watan farko da maraice a cikin jejin Sinai bisa ga dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa. Haka kuwa Isra'ilawa suka yi.
6 Akwai waɗansu mutane da suka ƙazantu ta wurin taɓa gawar wani mutum,don haka ba su iya kiyaye Idin Ƙetarewar a ranar ba. Sai suka zo wurin Musa da Haruna a ranar,
7 suka ce masa, “Ai, mun ƙazantu saboda mun taɓa gawa. Me ya sa aka hana mu mu ba da hadaya ga Ubangiji tare da sauran 'yan'uwanmu a ƙayyadadden lokacin yinta?”
8 Sai Musa ya ce musu, “Dakata, har na ji abin da Ubangiji zai umarta a kanku.”
9 Ubangiji kuwa ya faɗa wa Musa