3 Yahuza kuwa ya ce wa Saminu ɗan'uwansa, “Ka zo tare da ni a wurin da aka ba ni rabon gādona don mu yaƙi Kan'aniyawa, ni kuma zan tafi tare da kai a wurin da aka ba ka rabon gādonka.” Saminu ya tafi tare da shi.
4 Yahuza ya tafi, Ubangiji kuwa ya ba da Kan'aniyawa da Ferizziyawa a gare su, suka kashe mutum dubu goma daga cikinsu a Bezek.
5 Suka iske Adoni-bezek a can, suka yi yaƙi da shi, suka kuma ci Kan'aniyawa da Ferizziyawa.
6 Sai Adoni-bezek ya gudu, amma suka bi shi, suka kama shi. Suka yanyanke manyan yatsotsinsa na hannu da na ƙafa.
7 Ya kuma ce, “Sarakuna saba'in waɗanda aka yanyanke manyan yatsotsinsu na hannu da na ƙafa, suka kalaci abincinsu a ƙarƙashin teburina. Allah kuwa ya yi mini kamar yadda na yi musu.” Suka kawo shi Urushalima, a nan ya mutu.
8 Mutanen Yahuza kuwa suka yaƙi Urushalima, suka ci ta, suka karkashe mutanenta, suka kuma cinna mata wuta.
9 Bayan wannan suka gangara kuma, suka yaƙi Kan'aniyawan da suke zaune a ƙasar tudu, da Negeb, da filayen kwari.