20 Tsohon nan ya ce, “Ku zo mu je gidana, duk abin da kuke bukata zan ba ku, amma kada ku kwana a dandalin.”
21 Sai ya kai su gidansa, ya ba jakan harawa, aka wanke ƙafafun baƙin, sa'an nan suka ci suka sha.
22 Sa'ad da suke cikin jin daɗin ci da sha, 'yan iskan da suke birnin suka zo suka kewaye gidan, suka yi ta bubbuga ƙofar, suka ce wa tsohon, “Ka fito mana da mutumin da ya zo gidanka don mu yi luɗu!”
23 Tsohon kuwa ya fito wurinsu, ya ce musu, “A'a, 'yan'uwana, kada ku yi mugun abu haka, wannan ya sauka a gidana, kada ku yi wannan rashin kunya.
24 Ga 'yata budurwa da ƙwarƙwararsa, bari in fito muku da su, ku yi abin da kuka ga dama da su, amma kada ku yi wa mutumin nan wannan abin kunya!”
25 Amma 'yan iskan ba su yarda ba, sai Balawen ya fitar da ƙwarƙwararsa gare su. Suka yi mata faɗe, suka wulakanta ta dukan dare har kusan wayewar gari, sa'an nan suka ƙyale ta.
26 Da gari ya waye, ƙwarƙwarar ta zo ta fāɗi a ƙofar gidan tsohon, inda maigidanta ya sauka, tana nan har hantsi ya cira.