7 Dukanku nan Isra'ilawa ne, me za mu yi a kan wannan al'amari?”
8 Dukan jama'a kuwa suka tashi gaba ɗaya, suna cewa, “Daga cikinmu ba wanda zai koma alfarwarsa ko kuwa gidansa.
9 Wannan shi ne abin da za mu yi wa Gibeya, mu zaɓi waɗansunmu su fāɗa mata da yaƙi.
10 Kashi ɗaya daga goma na Isra'ilawa su ba da abinci ga sojoji. Sauran jama'a kuwa su je su hukunta Gibeya saboda muguntar da ta aikata cikin Isra'ila.”
11 Saboda haka dukan mutanen Isra'ila suka taru niyya ɗaya domin su fāɗa wa garin da yaƙi.
12 Kabilar Isra'ila kuwa suka aiki manzanni ga kabilar Biliyaminu suka ce, “Wace irin mugunta ce wannan da kuka aikata?
13 Yanzu sai ku ba da mutanen nan 'yan iska da take cikin Gibeya don mu kashe su, mu kawar da mugunta daga cikin Isra'ila.” Amma mutanen Biliyaminu ba su kula da maganar 'yan'uwansu, Isra'ilawa ba.