13 Sa'an nan taron jama'a suka aika wa mutanen Biliyaminu da suke a Dutsen Rimmon, cewa, yaƙi ya ƙare, sai salama.
14 Mutanen Biliyaminu kuwa suka komo, aka ba su budurwan nan da aka bar su da rai aka kawo su Yabesh-gileyad, amma budurwan ba su ishe su ba.
15 Sai mutanen suka yi juyayin mutanen Biliyaminu domin Ubangiji ya naƙasa kabila daga kabilar Isra'ila.
16 Saboda haka dattawan taron jama'a suka ce, “Ƙaƙa za mu yi da waɗanda suka ragu da ba su sami mata ba, da yake an hallaka matan kabilar Biliyaminu?”
17 Sai suka ce, “Tilas, waɗanda suka ragu daga mutanen Biliyaminu su sami gādo domin kada a shafe kabila daga cikin Isra'ila,
18 amma fa ba za mu iya aurar musu da 'ya'yanmu mata ba.” Sun faɗi haka ne kuwa, domin sun riga sun rantse cewa, “Duk wanda ya aurar da 'yarsa ga mutumin Biliyaminu la'ananne ne.”
19 Suka kuma ce, “Ga shi, idin Ubangiji na shekara shekara a Shilo ya kusa.” (Shilo tana arewacin Betel, kudu da Lebona, gabas da hanyar da take tsakanin Betel da Shekem.)